Type Here to Get Search Results !

Main event

Na fi Buhari cancanta don na fi shi ilimi - Dan takarar shugaban kasa a PDP - Kabiru Tanimu


Turaki, babban lauya mai lambar SAN, ya ce ya fi Buhari cancanta ne saboda ya fi shi ilimin boko. Tsohon minista a lokacin mulkin jam'iyyar ta PDP karkashin Goodluck Jonathan, Tanimu Turaki na daga cikin mutane 7 da suka bayyana sha'awar takara domin gwabzawa da shugaba Buhari.

Turaki, Dan asalin jihar Kebbi, ya bayyana cewar akwai fahimtar juna tsakanin masu son yiwa jam'iyyar ta PDP takara, a saboda haka ya ce ba za a fuskanci kowacce matsala ba duk wanda a karshe ya samu nasarar a zaben fitar da dan takara. A shekarar 2015 ne jam'iyyar APC ta kayar da gwamnatin PDP bayan ta shafe 16 tana mulkin Najeriya.

Jam'iyyar PDP na saka ran sake komawa kan karagar mulkin Najeriya a zaben shekarar 2019 mai zuwa. 'Yan jam'iyyar APC mai mulki na cigaba tsallakawa zuwa jam'iyyar PDP, wani lamari dake karawa jam'iyyar ta PDP karfin gwuiwar ganin cewar zata iya samun nasara a zaben na shekarar 2019.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies