Jihar Kebbi, Gwamna Bagudu da mataimakinsa sun kaura zuwa Ekiti, wa ke tsaron gida ?

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 10-7-2018


Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu wanda shi ne shugaban kwamiti da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada bisa amana, domin ya shugabanci wani kwakkwarar kwamitin jam'iara APC wadda za ta fuskanci zaben Gwamna da ake shirin yi a jihar Ekiti, wacce take tamkar gasar kwallon kafa na kasashen Duniya tsakanin jam'iyar PDP wacce ke kan mulki da kuma jam'iyar APC wacce ke neman kayar da Gwamna mai ci Ayodele Fayose.

Sakamakon haka, Gwamna Bagudu ya dau harama tare da tawagarsa daga jihar Kebbi, suka yi ma Ado Ekiti tsinke. Bayanai da muka samu, an tabbatar da cewa tawaga fa ta jihar Kebbi ta isa wannan birni lafiya kalau kuma kowa na cikin koshin lafiya.

Haka zalika, tawagar ta kunshi wakilai daga fadin jihar Kebbi, musamman daga Masarautu hudu da ke fadin jihar.

Amma wannan yana faruwa ne fa yayin da jama'ar jihar Kebbi musamman Ma'aukatan gwamnati suke tsammanin biyan albashi ganin cewa an biya albashin watan da ta wuce a tsakiyar wata.

Bincikenmu ya bayyana cewa, wasu Ma'aikatan ma, tsammani sukeyi cewa za' a biya kudade na ayyukan yau da kullum ganin cewa ana zargin cewa ba'a biya ba a wata da ta  gabata, watau cash allocation.

Yayin da wannan ke faruwa, sai ga labarin cewa mataimakin gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe ma ya dira a can Ado Ekiti duk da kasancewa Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu yana cikin Ado Ekiti.


Sakamakon haka muka tuntubi wani masani harkar tsaro kan lamarin wanda ya bayyana mana cewa , kasancewa Gwamna da mataimakinsa su bar jiha a lokaci daya ba wani laifi bane, amma bai cancanta da tsarin ingancin tsaro ba.

Bayan gagarumin wakilci daga Gwamnan jihar Kebbi Atiku Baguda wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa Buhari kan harkar zaben na Ekiti, ga kuma tawaga mai karfi daga jihar Kebbi wanda ta kunshi manyan 'yan siyasa na jihar Kebbi daga jam'iyar APC.

Wata tambaya a nan ita ce, ko ya zama wajibi mataimakin gwamnan Kebbi ya kasance cikin wannan tafiya ganin cewa Gwamna tare da wakilai daga jihar Kebbi suna cikin wannan tawagar ?.

Yanzu haka , Gwamna tare da mataimakinsa basu cikin jihar Kebbi, domin sun dira jihar Ekiti saboda su ceto jam'iyar APC domin ganin ta lashe zaben Gwamna da za'a yi a fadin jihar ta Ekiti.

SANARWA

Seniora Tech tana FLASHING ko cire SECURITY, Makullin waya a N500 kacal, wannan garabasa ce ga 'yan uwan mu a garin Birnin kebbi da kewaye tare da ilahirin jama'ar jihar Kebbi.

Muna shago mai lamba 50 hawa na sama a TAUSHI PLAZA yamma da gidan Wazirin Gwandu Marigayi Malam Umaru, Titin Ahmadu Bello a garin Birnin kebbi.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN