Buba Galadima, shugaban kungiyar sabuwar APC, yace kungiyar
ta fi yawan mutane a majalisar dokoki da za su tsige shugaban kasa Muhammadu
Buhari. A cewar jaridar Thisday, Galadima ya bayyana hakan ne yayinda yake
maida martani ga Adams Oshiomhole wanda ya bayyana R-APC a matsayin harsuna yan
baranda. Oshiomhole ya bayyana hakan ne bayan tattaunawar da yayi da masu ruwa
da tsaki na APC a majalisar wakilai
A baya NAIJ.com ta rahoto cewa matasa a Kano karkashin wata
kungiyar siyasa mai suna ‘Ranar Wanka Buhari/Ganduje Progressive Group’, sun
kammala shirye-shirye don yin gangamin matasa miliyan uku a jihar domin nuna
hamayya da ayyukan siyasa na gammayar kugiyar da sabuwar APC wato Reformed APC (R-APC).
Da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis, shugaban kungiyar,
Alhaji Bala Salihu Dawaki, ya ce kwanan nan za su gudanar da tattakin, a
cewarsa, an kammala shirye-shirye.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>>
https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
hausa.naij.ng