• Labaran yau


  Halin bera ya janyo ma wata Jaruma gurfana a gaban Kotu kan satar kayakin N7m

  Fitacciyar Jarumar Nollywook kuma mai shirya Finafinan Yarbanci watau Yetunde Akilapa, ranar Alhamis, ta gurfana a gaban wata Kotun Majistare a birnin Lagos bisa zargin aikata sata na dukiya da ya kai N7m.

  An gurfanar da Jarumar wacce ke zaune a gida mai lamba 7, unguwar Oladelola da ke Ketu a jihar ta Lagos bisa zargin sata tare shiga gida ba tare da izini  ba. Inda daga bisani ta saci wasu gwalagwalai da sarkoki masu daraja na zinari da azurfa.

  Amma Jarumar bata amsa laifin ta ba a gaban Kotu.

  Jarumar ta yi tashe a wani Fim na Yarbanci a 2013 “Ileri-Oluwa’’ wanda shi ne bakandamiyarta kuma sanadin samun daukaka a wajenta. Amma bayanai sun nuna cewa tun azil, Jarumar ta sha fama da matsaloli inda ake ganin ta fada rigingimu da suka jibanci aikata sata a can baya a rayuwarta

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>>

  https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com

  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa

  08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Halin bera ya janyo ma wata Jaruma gurfana a gaban Kotu kan satar kayakin N7m Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama