Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa
watau EFCC za ta taso Gwamnan Ekiti Ayo Fayose a gaba. Hukumar ta EFCC ta fara
kakkabe takardun ta domin fara binciken badakalar da ke kan Fayose
EFCC na zargin Fayose da laifuffuka da dama Dazu ne dai
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa barna ta tabbatar da cewa watan
damke Gwamna Ayodele Fayose ya kusa kankama. Ana zargin Gwamnan da karkatar da
kudin Jihar sa wajen gina gidan gona. EFCC dai tana jira ne kurum Gwamnan ya
sauka daga kujerar sa ta yi ram da shi. Dokar kasa ba ta bada dama a bincike
Gwamna da Shugaban kasa ba muddin su na kan mulki. Kwanan nan ne Fayosen zai
mika mulkin Jihar.
Mun ma ji kishin-kishin din cewa Gwamnan mai shirin ajiye
ragamar mulki ya fara shirin barin Najeriya. Ana rade-radin cewa tuni har
Gwamnan yayi fasfo ya kuma saye tikitin jirgi domin tserewa daga Najeriya
kwanan nan. EFCC tayi wannan jawabi ne ta shafin ta na Tuwita inda ta ce ta na
sa ran haduwa da Gwamnan kwanan nan. A jiya ne ‘Dan takarar Jam’iyyar APC
Kayode Fayemi ya doke Jam’iyyar PDP ta su Fayose ya lashe kujerar Gwamnan
Jihar. Dazu kun ji cewa Gwamna Ayo Fayose ya koka da yadda aka gudanar da zaben
Gwamnan Jihar Ekiti. Ayo Fayose da ke shirin ajiye mulki ya zargi ‘Yan Sanda da
murde zaben Gwamnan Jihar.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Tags:
LABARI