Birnin kebbi: 'Yansanda sun ceto Sadiya matar Anas Sha'aban da aka sace

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 8-7-2018


'Yansandan jihar Kebbi sun yi nassarar kubutar da wata mata mai juna biyu, Hajiya Sadiya Tsoho, matar Malam Anas Sha'aban daga hannun masu satar mutane. An sace Sadiya a mako da ya gabata a gidanta da ke garin Birnin kebbi.Sadiya mata ce ga Anas mai wani katafaren kasuwar zamani da ke unguwar Nassarawa a Birnin kebbi.

Sanarwar ceto Sadiya ta fito ne daga bakin kakakin hukumar 'yansanda na jihar Kebbi DSP Mustapha Suleiman kamar yadda kampanin dillacin labarai ta Najeriya NAN ta ruwaito.

DSP Mustapha ya ce ba'a biya kudin fansa ba kafin a saki Sadiya daga hannun wadanda suka sace ta. Ya kuma kara da cewa bayan an sace Sadiya, an kai ta wani Hamada da ke yankin garin Mahuta , a karamar hukumar Fakai da ke kudancin jihar Kebbi.

Wata majiya ta ce mutanen sun labe a wani waje a kusa da gidansa da ke unguwar Rafin Atiku har tsawon awanni, ranar 1 ga watan Juli. Amma da yake bai zo ba, sai suka nufi gidansa suka tarar da matarsa mai juna biyu kuma suka yi awon gaba da ita. 

Bayan haka ne majiyar ta ci gaba da cewa, sai mutanen suka tuntubi iyalanta suka nemi kudin fansa naira Miliyan dari biyu N200m kafin su sake ta.

Bayanai sun tabbatar cewa duk iya kokarin da manema labarai suka yi domin su sami Anas Sha'aban mijin Sadiya domin jin ta bakinsa dangane da lamarin ya ci tura, domin cewa ake yi masu ai bayanan.

DSP Suleiman ya ce duk da yake ba wanda aka kama daga cikin wadanda suka sace Sadiya kawo yanzu, amma tuni Sadiya ta koma gida kuma ta sadu da iyalinta cikin koshin lafiya.

SANARWA

Seniora Tech tana FLASHING ko cire SECURITY, Makullin waya a N500 kacal, wannan garabasa ce ga 'yan uwan mu a garin Birnin kebbi da kewaye tare da ilahirin jama'ar jihar Kebbi.

Muna shago mai lamba 50 hawa na sama a TAUSHI PLAZA yamma da gidan Wazirin Gwandu Marigayi Malam Umaru, Titin Ahmadu Bello a garin Birnin kebbi.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN