Shugaban tsagin sabuwar Jamiyyar APC mai lakabin rAPC Alhaji
Buba Galadima, ya bayyana yadda abubuwa su ka same shi a dalilin shugaban kasa
Muhammad Buhari.
Buba Galadima wanda tsohon makusancin shugaban kasa Buhari
ne, ya bayyana cewa sau 38 ana garkame shi akan yana tare da Muhammadu Buhari,
ya kara da cewa sau 5 ana yi masa tayin mukamin Minista amma yayi biris da
tayin. Ya fadi hakan ne a lokacin da ya bakunci wani shiri da gidan talabijin
na AIT yake a gabatarwa a kowacce Asabar. Sannan ya kuma ce yanzu wadanda su ke
cikin gwamnatin shugaba Buhari yan ta fadi gasassa ne, domin 'yan ciranin
siyasa ne. "Bani da wata matsala da Shugaba Buhari, domin kuwa tun daga
watan janairun Shekarar 2002 na ke taimakonsa akan ya zama shugaban kasa. Domin
na ba shi gudummawar da ko shi kan sa bai baiwa kansa ba, kuma babu wani dan
kasar nan da zai iya wannann sadaukarwar" in ji Buba Galadima
Ya cigaba da cewa, "A dalilin shugaba Buhari na
fuskanci tuhuma, dauri da kuma cin zarafi, kai har daure ni aka yi sau 38, amma
hakan bai tsaya iya nan ba, domin kuwa har daure ne aka yi tamau tare da
garkameni".
A karshe kuma ya bayyana takaicinsa dangane da yadda wasu
mutane su ka kewaye shugaba Buhari, wadanda a baya su ne suke bayar da kudi
domin ganin burinsa na mulkin kasar nan bai kai ga nasarar ba. Da ya ke bayani
a kan dangantakarsu da shugaba Muhammad Buhari bayan an kammala zaben 2015, ya
ce jim kadan da kaiwa ga nasarar zaben, sai shugaba Buhari ya yi taro da manema
labarai na duniya, inda ya bayyana cewa ba shi da bukatar kuri'ata da ta magoya
bayana da ta kuma iyalina da ma ta sauran duk wanda ya ke tare da ni. A karshe
Buba Galadima ya tofa albarkacin bakin sa akan yaki da cin hanci da rashawa da
gwamnatin shugaba Buhari ta keyi, inda ya ce; "Wannan yana a matsayin wasa
da Hankalin ne kawai, ya kamata gwamnati da ta sauya fasali da tsarin yadda ta
ke yi akan yaki da cin hanci da rashawa"
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
hausa.naij.ng