Wakilin isyaku.com
Alummar unguwar Nassarawa 1 Birni kebbi sun koka bisa yadda barayi
suka addabe su da satar wayoyin salula da dare. Wata majiya ta shaida
mana cewa yanzu haka, an shiga wasu gidaje a daren Talata kuma aka
yi awon gaba da wayoyin salula.
Haka zalika, bayanai
sun nuna cewa hatta Shiyar Sarakuna ma barayi sun hare su inda kwana uku
da suka gabata ma barayi sun shiga wasu gidaje kuma suka saci
wayoyin salula.
Sannu a hankali an fara samun kalubale a fannin tsaro a cikin garin Birnin kebbi, sakamakon yadda yawan sace
sacen wayoyin salula a gidajen mutane ya karu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira