• Labaran yau


  Bamu taba samun shugabancin majalisar dattawa mai munin na Saraki ba - El-rufai


  Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da ambatan sunayen wasu mambobin majalisar All Progressives Congress (APC) cikin wadanda suka sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP) ba tare da yardarsu ba.

  El-Rufai yayi ikirarin cewa wasu daga cikin Sanatocin da Saraki ya ambata sun fito daga baya sunce ba sauya sheka za su yi daga APC ba sannan kuma basu san dalilin da yasa aka sanya sunayensu cikin masu sauya shekar ba, jaridar The Cable ta ruwaito. Gwamnan wadda yayi magana a wata hira da wasu tashoshin radiyo a Kaduna a ranar Alhamis,ya ce majalisar dattawa karkashin jagorancin Bukola Saraki shine mafi muni da Najeriya ta taba yi.

  El-Rufai ya kuma daura laifin rashin kammala ayyukan da ake yi a jiharsa akan Sanata Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da kuma Danjuma Laah.

  El-Rufai ya ce rashin amincewa da sanatocin suka yi wajen ciwo bashin dala miliyan 350 daga bankin duniya zuwa jihar shine ya haddasa rashin kammaluwan aikin.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bamu taba samun shugabancin majalisar dattawa mai munin na Saraki ba - El-rufai Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama