A yau Juma'a, Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da wasu manyan
sauye-sauye da tayi wa manyan kwamandojin ta da ma wasu ma'aikatan.
Sabbin canjin da akayi ya shafi Kwamandan Operation Lafiya
Dole dake Arewa maso Gabashin Najeriya da Kwamandan Jami'an tsaron hadin gwiwa
(JTF). Jami'an da aka yiwa sabbin naddin za su kama aiki ne a ranar 1 ga watan
Augustan wannan shekarar. A sanarwar da ta fito daga hannun Direktan Hulda da
Jama'a na Sojin, Brig. Janar Texas Chukwuma, ya yi bayanin cewa an dauki
matakin ne don kawo sabbin hannu cikin Operation Lafiya Dole don cinma burin
Shugaban Sojin Najeriya, Lafatant Tukur Yusuf Buratai.
Sai dai wata majiya daga Hukumar Sojin tace shaidawa Daily
Trust cewa canjin ba zai rasa nasaba da kissar da 'yan ta'adda da bata gari ke
yiwa sojoji a wasu sassan kasar nan.
Wadanda aka yiwa naddin sun hada da; Manjo Janar AM Dikko
wanda zai kama aiki a matsayin Kwamandan Operation Lafiya Dole, sai Brig. Janar
AO Abdullahi da zai fara aiki a matsayin Kwamandan Sector 2 na Operation Lafiya
Dole sai Brig. Janar UU Bassey a matsayin Kwamandan Sector 3 na Operation
Lafiya Dole. Saura sun hada da Manjo Janar CO Ude a matsayin Kwamandan JTF
Ndjamena, sai Manjo Janar J Sarham a matsayin Babban kwamandan 6 Division da
kuma Manjo Janar EB Kabuk a matsayin Babban Kwamandan 82 Division.
Manjo Janar MS Yusuf shi kuma zai kama aiki a matsayin
Babban Kwamandan 81 Division da Manjo Janar BA Akinroluyo a matsayin Kwamandan
3 Division. Sanarwan kuma tace cikin manyan jami'an Sojin da canjin ya shafa
sun hada da Manjo Janar Leo Irabor wanda zai kama aiki a matsayin Shugaban
horaswa da ayyuka a Hedkwatan tsaro yayin da Manjo Janar LO Adeosun zai fara
aiki a matsayin Shugaban horaswa da ayyuka a Hedkwatan Sojin Kasa. Sauran da sauyin
ya shafa sun hada da Manjo Janar JE Jakko da Manjo Janar AB Abubakar da Manjo
Janar A Mohammed da Manjo Janar LKJ Ogunewe.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng