Type Here to Get Search Results !

'Yansandan Kebbi sun rafto masu fashin mota a yankin Yamma mai nisa


Hukumar yan sandan jihar Kebbi tayi nasarar cafke wani barawon motoci wanda ya Kware a satar motoci a jihar. Yan sanda sunce wanda ake zargin yana zuwa daga Ilorin ne, jihar Kwara satar ababen hawa. Wanda ake zargin, Peter James, wanda Dan asalin kasar Ghana ne, an kama shi a birnin Kebbi a lokacin da yake kokarin guduwa da wata mota kirar Toyota Camry. A dubawar da manema labarai sukayi wa wanda ake zargin da kuma sauran masu laifi a shelkwatar yan sandan jihar dake birnin Kebbi, kwamishinan yan sandan jihar, Kabiru Ibrahim yace wanda ake zargin ya dade yana sace motoci yan guduwa dasu inda yake siyar dasu

Barawon motar an taba kama shi kuma an tuhume shi, inda daga baya kotu ta sake shi. Amma bayan satittika kadan aka kara kama shi da laifin satar mota. A lokacin da wanda ake zargin ke amsa tambayoyi daga manema labarai, yace shi ba satar motar yayi ba, siyan ta yayi Naira 800,000 daga wani. Kwamishinan yan sandan yace za a cigaba da bincike sannan a tura shi kotu.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN