Kamar kowane dan siyasa, Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin
yakin neman zabe a shekarar 2015 ya zagaya jahohin Najeriya tare da kuma ganawa
da daruruwan kungiyoyi inda ya yi masu alkawurra da dama idan dai har suka zabe
shi.
Duk da dai siyasa daman kamar yadda masu fashin baki da dama
kan fada cewa ta gajin rashin cika alkawari, amma talakawan Najeriya da ma
al'ummomin kasashen duniya sun yi ammanar cewa shugaba Buhari ya sha ban-ban da
sauran 'yan siyasa.
1. Magance rashin tsaro:
Duk da dai a iya cewa gwamnatin sa
ta samu nasara sosai musamman ma a yakin da take yi da 'yan kungiyar Boko
Haram, har yanzu akwai sauran rina a kaba a sassan kasar.
2. Farfado da tattalin arzki:
Da samun karayar darajar kudin
naira tare kuma da hauhawar farashin kayan masarufi da na abinci, masana da
dama na ganin yanzu tattalin arzikin Najeriya kara tabarbarewa yayi.
3. Samar da aikin yi ga matasa:
Duba da irin shire-shiren da
gwamnatin ta bullo da su da ke da alaka ta kai tsaye ga samarwa matasa aikin yi
kamar su shirin nan na N-power da kuma harkar noma, a iya cewa gwamnatin ta
kokarta. Amma dai saboda yawan al'ummar kasar, har yanzu rashin aikin yi a
tsakanin matasa na nan ba'a magance shi ba.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng