An tsaurara tsaro a titin Independent wacce ke wucewa ta kan babbar Kotun tarayya inda ake sa ran za'a gurfanar da Sheikh El-Zakzaky tare da Matarsa bisa wasu laifuka da gwamnatin jihar Kaduna ta ke tuhumarsa da aikatawa.
Amma wata majiya da bata son a fadi sunanta ta shaida wa Daily Trust cewa Alkalin da zai saurari shari'ar ba zai sami halartar Kotun ba domin ya sami hadari da dare.
Majiyar ta kara da cewa wata Keke napep ce ta buge shi yayin da yake kokarin ketarawa domin ya shiga shagon wani mai yi masa aski.
Sakamakon rashin samun halartar Alkalin a zaman Kotu a yau, an dage shari'ar har zuwa ranar 11 ga watan Yuli, 2018.
Amma wani faifan bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda wasu da ake zargin cewa 'yan Shi'a ne da suka fusata sun yi ma wani jami'in 'dansanda ruwan duwatsu har ya mutu tare da barnata wata mota ta 'yansanda .
Tuni dai wata babbar Kotun tarayya a birnin Abuja ta bayar da belin shugaban mabiya Shi'a na Najeriya Sheikh Ibrahim El-zakzaky, amma mahukunta suka yi kunnen uwar shegu da umarnin Kotun kuma suka ci gaba da tsare shi.
Kalli yada aka yi ma dansanda ruwan duwatsu:
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com