Tun da farko a cewar Muhammed ya gargadi Usman da
hawainiyarsa ta kiyayi ramar matar da zai aura don kuwa har yayi tambaya amma
Usman din yaki ji balle ya saurara. Sannan ya bayyanawa ‘yan sanda cewa ya
dauki matakin ne domin yayi duk mai yiwuwa don ganin usman din ya kyale masa
matar da yake mutukar son aura, kuma ko kusa ba ya nadamar wannan aika-aika da
yayi.
“Ba na nadamar abinda na aikata saboda inda ban kashe shi a
lokacin ba da ni zai kashe, gara ya tafi can don kar ma ya sake hada hanya da
ni” “Ban yi aure ba, kuma ban damu da duk matakin da zai biyo baya ba, abu mai
muhimmanci kawai shi ne nayi maganinsa daga shiga sabga ta. Akwai mata da yawa
amma sai ya zabi ya cigaba da neman matar da na riga da nayi tambayar aurenta,
hukuncin da na dauka shi ne ya dace da shi”. Baba ya jaddada.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Muhammad Abubakar ya
bayyana cewa wanda ake zargin ya aika wani yaro ne mai suna Abdul ya siyo masa
kwalba uku na fetir wanda yayi amfani da shi wajen babbaka abokin neman
budurwar tasa. Abubakar ya ce anyi sauri an garzaya da wanda iftila’in ya faru
da shi cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) dake
Bida daga basani kuma aka
mayar da shi zuwa asibitin Gwagwalada na Abuja inda ya cigaba da karbar magani
kafin daga bisani rai yayi halinsa. Kuma za’a kai maganar gaban alkali da zarar
an kammala bincike.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng
Tags:
LABARI