Rashin bayyanar mai shari’a Gideon Kurada domin sauraren
shari’ar shugaban mabiya mazabar Shi’a El-Zakzaky da matarsa da ya gamu da
cikas a dalilin rashin bayyanar alkalin
Gwamnatin jihar Kaduna dai ta zayyana laifuka takwas da take
tuhumar Ibrahim El-Zakzaky da matar shugaban mabiya Shi’an na Najeriya. Daga
cikin laifukan da ake zarginsu da shi sun hada da hada baki wajen kulla
kitsattsiya da kin yin katabus gami da tabuka komai wajen kare faruwar rasa rayukan
mutane da sauransu.
Amma sai dai an hana ‘yan jarida shiga cikin harabar kotun
domin shaida yadda zaman kotun zai kasance. Lauyan wanda ake kara (Zakzaky)
Femi Falana (SAN), ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa,
alkalin yana sane ya ki halartar kotun domin sauraren shari’ar A saboda haka ne
lauyan wanda ake kara da kuma lauyan mai karewa sun cimma matsayar dage zaman
zuwa 11 ga watan Yuli domin cigaba da shari’ar.
Falana ya kuma nuna ganin baiken jami’an ‘yan sanda na
dakatar da ‘yan jarida daga shiga kotun domin ganin yadda zaman zai kaya, domin
kuwa a cewarsa babu wata doka da ta hana mutane shaida zaman kowacce shari’a.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng
Tags:
LABARI