Cikin wani rahoto mai kunshe da ban al'ajabi ya bayyana
cewa, wani matashin mutum ya kashe kansa yayin da ya jefo kansa tun daga saman
bene na kololuwa dake babban Masallaci mai alfarma na Birnin Makkah a can Kasar
Saudiyya.
Hukumomin tsaro na Kasar Saudiyya sun bayyana cewa, wannan matashin
mutum da ya ziyarci kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Umarah a wannan wata
na Ramadana ya mutu ne nan take yayin da ya fado kasa da misalin karfe 9.20 na
daren ranar Juma'ar da ta gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan matashi bai wuci shekaru
26 a duniya ba kuma dan asalin kasar Faransa ne da ya yi tsarki na shiga
addinin Islama kamar yadda wata jarida ta kasar Taki, Daily Sabah ta bayyana.
kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, wannan ba shine
karo na farko da wani mahaluki ya yi yunkurin kashe kansa a harabar Masallaci
mai Alfarma daura da Dakin Ka'aba duk da cewar kisan kai a addinin Islama yana
daya daga cikin manyan laifuka na kololuwa da ba bu yafiya ga duk wanda ya
aikata hakan.
An garzaya da gawar wannan Matashi zuwa asibiti domin binkicen
dalilin da ya sanya ya yankewa kansa wannan mummunan hukunci tare da binciken
yadda ya aikata hakan.
A shekarar da ta gabata ne wani mutum dan kasar ta
Saudiyya ya yukurin kashe kansa ta hanyar bankawa kansa wuta a gaban dakin
Ka'aba yayin da jami'an tsaro suka yi gaggawar hana shi.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#hausa.naij.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI