Ban so aka mayar wa Obasanjo da martani ba - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bai so aka mayar da martani ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba.

Shugaba Buhari ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da mambobin kungiyar da ke goyon bayansa wato (Buhari Support Organisation BSO) a fadarsa a Abuja a daren Juma'a.

Sai dai kuma duk da Shugaban ya ce ministan watsa labarai da al'adu Alhaji Lai Muhammad "ya saba ma shi" a martanin da ya mayar wa Obasanjo amma kuma ya yaba da yadda aka mayar da martanin.
Shugaban ya kuma ce shi ya hana mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya mayar da martanin saboda shi ba sa'an Obasanjo ba ne.

A ranar Juma'a ne tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar da sanarwa yana zargin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kokarin kama shi.

Mista Obasanjo ya ce gwanatin Buhari na tattara shaidun boge domin ta daure shi saboda sukar da yake wa shugaban, inda ya ce rayuwarsa na cikin hatsari domin an kwarmata ma sa cewa yana cikin jerin sunayen mutanen da ake farauta.

A martanin da ya mayar, ministan watsa labarai da al'adu Alhaji Lai Muhammad ya ce "gwamnatin Buhari ba za ta damu da wasu zarge-zargen da ba su da ma'ana ba, daga ko wane bangare da nufin karkatar da hankalinta ga ayyukan da ta ke."

Ya kara da cewa: "wadanda ke da kashi a jiki ne ya kamata su ji tsoro, marar laifi ba zai damu da wani bincike ba, a zahiri ko a mafarki".

"Hankalin gwamnati ya karkata ne ga kokarin gyara barnar da PDP ta yi a shekaru 16 kamar yadda ta fi mayar da hankali ga ci gaba da gina nasarorin da ta samu a shekaru uku" in ji Lai Muhammad.

Shugaba Buhari ya ce "martanin da ministan ya mayar ya nuna wa 'yan Najeriya ainihin abin da ya faru a lokacin da suka karbi mulki a 2015 da kuma kokarin da gwamnatina ke yi na farfado da tabarbarewar tattalin arzikin da ta gada."

Ya kuma ce "lokacin da Obasanjo ya rubuta wasika, Femi Adeshina ya ta yunkurin gaggawar mayar da martani amma na dakatar da shi saboda dalilai guda biyu: Na farko shi ba sa'a na ba ne da kuma Obasanjo.

"Na biyu kuma gidan soja guda muka fito da Janar Obasanjo, don haka ba zan yarda ta shafi shi ba (Adeshina) kuma na bari ya mayar da martani. Amma Lokacin da Lai Mohammed ya zo na hana shi amma ya nace."

Shugaban ya ce ya fahimci aikin Lai Mohammed ya yi kyau saboda yadda mutane da yawa suka kira suna yaba ma sa.

Shugaban na Najeriya ya kuma kalubalanci 'yan adawa cewa su bincika daga Amurka da Turai zuwa Asiya, tsakanin 1999 zuwa 2014, shekarun da PDP ta yi tana mulki, ana samar da gangar danyen mai miliyan 2.1 a rana akan dala 100 duk ganga.

Ya ce da gangan ya ki tube gwamnan Babban Bankin Najeriya domin yana son ya ba shi dama ya farfado da halin da tattalin arzikin kasar yake ciki.

Takun saka ya zafafa tsakanin shugabannin biyu tun bayan da Mr Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya yi Allah-wadai da yadda yake gudanar da mulki, sannan ya ce bai cancanci a sake zabarsa ba a zaben 2019.

A kwanakin baya Buhari ya zargi gwamnatin Obasanjo, wanda ya mulki kasar a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007, da "kashe dubban daloli kan wutar lantarki ba tare da an ga wutar a kasa ba". Obasanjo ya musanta wannan zargi
  • Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015
  • A watan Janairun 2018 ne Obasanjo ya bukaci Buhari kada ya nemi wa'adin shugabanci na biyu
  • Obasanjo ya ce Buhari ya gaza inda ya bukaci ya sauka cikin mutunci bayan wa'adinsa na farko
  • A martaninta, gwamnatin Buhari ta ce ba za ta iya muhawara da Obasanjo ba
  • Ministan watsa labaria Lai Mohammed ya ce idon Obasanjo ya rufe ga nasarorin gwamnatin Buhari
  • Buhari da Obasanjo sun hadu a taron Tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Habasha a ranar 28 ga Janairu
  • A watan Afrilu Obasanjo ya jaddada cewa Buhari ya gaza wajen ciyar da Najeriya gaba.
  • Obasanjo ya ce bai kamata a sake zaben Buhari ba saboda gazawarsa.
  • Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa bayan ya caccaki gwamnatin Buhari
  • A ranar 22 ga Mayu Buhari ya soki gwamnatin Obasanjo kan lantarki
  • Buhari ya ce wani tsohon shugaban kasa ya kashe dala biliyan 16, kuma har yanzu ba lantarki
  • Obasanjo ya mayar wa Buhari da martani a ranar 22 ga Mayu
  • Obasanjo ya ce gwamnatin Marigayi Umaru 'Yar'adu ta kafa kwamitin bincike, kuma kwamitin ya wanke shi
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN