A makon nan ne mu ka samu labari cewa tashar bisar da aka
kaddamar farkon shekarar nan a Jihar Kaduna ta jawowa Najeriya makudan kudin da
su ka haura sama da Naira Biliyan 2.
Shugaban Hukumar tashar ruwa ta kan kudun da ke Kaduna KIDP
Tope Borisade ya bayanawa ‘Yan jarida a Legas cewa daga lokacin da aka bude
tashar a Watan Junairun nan zuwa yanzu an samu kudi har Naira Biliyan 2.
Mista Borisade ya kuma bayyana cewa Hukumar kwastam tayi wa
tashar lasisin daukar kaya. Bugu da kari ma dai yanzu babban bankin Najeriya
CBN sun san da zaman tashar ta kan tudu wanda ita ce ta farko a Yankin. A
wancan lokaci kun ji cewa tashar ta kan tudu za ta taimaka wa 'yan kasuwar da
ke Yankin Arewa wajen rage wahalhalun zuwa Kudu domin karbar kayansu ko fitar
da su zuwa waje ba tare da kashe kudin sufuri ta ruwa ba.
A bana ne Shugaba
Muhammadu Buhari ya bude tashar ruwa da ke kan tudu ta farko a Najeriya .
Wannan tasha ta na taimakawa 'yan kasuwar da ke Arewa da ke nesa da teku.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
hausa.naij.ng
Tags:
LABARI