Zaman zullumi a Kebbi kan hukunci da Kotu za ta yanke kan shari'ar Bagudu da Bello S. Yaki

Isyaku Garaba | Birnin kebbi | 28-6-2018

Sannau a hankali ranar 29/6/2018 ta gabato, sakamakon haka da yawa daga cikin jajayen wuya a cikin gwamnatin Sanata Atiku Bagudu suka dau haramar yi wa birnin Abuja dirar mikiya domin halartar babbar Kotun tarayya da za'a yanke hukunci kan shari'ar Gwamnan jihar Kebbi, a wata kara da aka shigar a kansa  dangane da harkar zaben da aka yi masa a matsayin Gwamna a 2015.

Tuni aka gan wasu manyan mukarraban Gwamna Atiku Bagudu, manyan jami'an gwamnati, tare da wasu fitattun 'yan siyasa na jam'iyar APC a jihar Kebbi suna haramar isa babban filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, da ke garin Ambursa domin darewa jirgin da zai yi dakon su zuwa Abuja, domin su shaida ido da ido yadda shari'ar za ta kasance a gobe Juma'a 29/6/2018, wacce ta ke kama da ranar hisabi a duniyar siyasar jihar Kebbi.

Akwai jita-jitar cewa an dauki naiyin wasu 'yan jarida guda biyu tare da wasu 'yan Social Media guda biyu wadanda aka biya masu kudin tikitin jirgi zuwa da dawowa daga Birnin kebbi zuwa Abuja domin su dauko labarin yadda shari'ar gobe Juma'a zata kasance.

Shekara uku kenan ana ta ja'in ja a Kotu har da tone-tonen asiri a gaban Kotu, tsakanin wasu fitattun 'yan siyasa  'yan asalin garin Birnin kebbi, Bello Sarkin Yaki da Atiku Abubakar Bagudu kan lamarin zabe na shekarar 2015, wanda sakamakon zaben ya ce Atiku Bagudu ne ya yi nassara, amma bangaren Bello S, Yaki wanda tsohon Janar na soja ne mai murabus suka hau kujerar na ki.

Sakamakon haka suka garzaya Kotu domin neman ganin an yi bicike a kan hujjoji da suke ganin cewa za su iya gamsar da Kotu domin Kotu ta cire Atiku Bagudu daga kujerar Mulki a ba Bello S.Yaki.

Wanna takaddama tsakanin manyan 'yan Siyasar guda biyu, ta haifar da bangaranci wanda ya rura wutar kiyayya tsakanin wasu 'yan asalin garin Birnin kebbi, kuma sakamakon haka ya haifar da kushe wa duk wani aiki da Atiku Bagudu ya yi a garin na Birnin kebbi inda wasu ke kwatanta aikin da ya yi da na tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari a matsayin ayyukan tsohuwar Gwamnatin Dakingari sun fi karko da aminci.

Wasu daga cikin misalai da ake bayarwa a kan wannan tsari shi ne yadda aka yi kwalbatoci a wasu unguwannin garin Birnin kebbi amma aka yi amfani da bulo marmakin kankare.

Sai dai wasu hanyoyi kamar yadda binciken mu ya tabbatar an yi su ne da kankare, musamman hanyar da ke wucewa daga Magamar bankin UBA zuwa Randabawul na Rima.

Ko ma da wace iri aka kwana, gari zai waye gobe Juma'a inda Alkalin Kotu zai yi carar Zakara domin farkar da masu barci guda biyu daga barci, a kan ko waye ya kamata ya kasance a cikin gidan haya mai alfarma na Gwamnatin jihar Kebbi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN