Sufeto Janar ya tsige Kwamishinan 'Yan sanda na Jihar Filato

Bayan kimanin tsawon sa'o'i 48 da kisan sama da mutane 100 a kananan hukumomin Barkin Ladi, Riyom, da Jos ta kudu a jihar Filato, Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya bayar da umarnin tsige kwamishinan 'yan sanda na jihar, Undie Adie kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana. Read more: https://hausa.naija.ng/1177284-kashe-kashen-jihar-filato-sufeto-janar-ya-tsige-kwamishinan-yan-sanda.html#117728Bayan kimanin tsawon sa'o'i 48 da kisan sama da mutane 100 a kananan hukumomin Barkin Ladi, Riyom, da Jos ta kudu a jihar Filato, Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya bayar da umarnin tsige kwamishinan 'yan sanda na jihar, Undie Adie kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana.Rahotanni sun bayyana cewa, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda Bala Ciroma dan asalin jihar Yobe, shine zai maye gurbin wannan kujera a jihar ta Filato. Wani takaitaccen rahoto na ranar Talatar da ta gabata da sanadin kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Matthias Tyopev ya bayyana cewa ba bu wani dalili dangane da tumbuke kwamishinan na 'yan sa

Bayan kimanin tsawon sa'o'i 48 da kisan sama da mutane 100 a kananan hukumomin Barkin Ladi, Riyom, da Jos ta kudu a jihar Filato, Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya bayar da umarnin tsige kwamishinan 'yan sanda na jihar, Undie Adie kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda Bala Ciroma dan asalin jihar Yobe, shine zai maye gurbin wannan kujera a jihar ta Filato. Wani takaitaccen rahoto na ranar Talatar da ta gabata da sanadin kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Matthias Tyopev ya bayyana cewa ba bu wani dalili dangane da tumbuke kwamishinan na 'yan sanda daga mukamin sa.

NAIJ.com ta fahimci cewa, a shekarar 1988 ne Kwamishina Ciroma ya kammala karatun digiri na farko a jami'ar Maiduguri, inda ya shiga makarantar koyan aikin 'yan sanda a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990. Ya rike makumai daban-daban yayin gumurzu bisa aiki cikin kusan duk rassa shida na kasar nan tare da rike babban mukami a hukumar han yiwa tattalin arziki zagon kasa.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN