Tarihi: Aleister Crowley, mutumin da ya fi kowa mugunta a fadin Duniya

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 26-6-2018


Tsarin shugabancin kungiyoyin asiri sun kasance cikin yanayi na bakin tsafi tun lokacin da suka wanzu a doron Duniya. Wannan ya kunshi zubar da jinin 'yan yara kanana da kuma jarirai. Wannan lamari ya kasance babban sirri da ba a son jama'a su sani, sai daga baya-bayannan kafin asiri ya fara tonuwa har jama'a suka fara sanin abin da lamarin ya kunsa.

Sakamakon haka, kimanin yara 400 ke bacewa a kowane shekara a kasar Amurka, yayin da yara 98.000 ke bacewa a kasar Britaniya ko U.K.

Fitaccen mutumin nan da Duniya ke nuni da shi a tari, kasancewa mutumin da ya fi kowa mugunta a fadin Duniya, watau Aleister Crowley shi ne mutumin da ya kirkiro  kungiyar asiri mafi shahara ta Freemasonry  da Golden dawn. Wannan mutum ya ce, " Yaro mai basira da baya da rigima shi ne wanda ya cancanta a mika jininsa ga tsafi"

Wani abin mamaki shine, kalaman Aleister Crowley da yake cewa "Yi abin da ka gan dama da rayuwarka" kalma ce da ta fito daga Benjamin Franklin, Franklin dan kungiyar asiri ne  wanda ya yarda da Shetan a matsayin ubangijinsa kuma wanda ke tsafi da jinin yara kanana.

Franklin yana zuwa wajen ibadar Shetan inda ake kira Klob na Wutan Jahannama .Manbobin wannan Klob sukan sha barasa, su kan sa karuwai su saka tufafin Chochi maza da mata, kuma su yi ta rungumar juna suna zina a tsakaninsu a kogon duwatsu, kuma suna bauta ma gumaka kamar Bacchus da Venus.


Fitaccen wakar nan ta mawaki Marilyn, "Misery Mechine" tana dauke da baitin " za mu yi sukuwa zuwa tsakiyar Thelema" amma fa wannan baiti a zahiri yana nufin za su yi sukuwa ne zuwa wajen bauta na Shetan Aleister Crowley.

Shi dai wannan mugun mutum a doron kasa, Aleister Crowley, yakan cin danyen kashi na karuwai a daidai lokacin da suke zinace zinace, shaye-shaye da rungume-rungume a wajen ibadarsu ta mujami'ar Shetan kamar yadda ya bayyana a wani faifen bidiyo na Tarihi mai take " IN SEARCH OF THE GREAT BEAST" wanda Daraktan wannan Fim Robert Garofalo ya jagoranta yayin da Lyn Beardsall ya tsara a 2007, ya ce Matar tsohon  shugaban Amurka George Bush, diya ce ga mutumin da ya fi kowa mugunta a Duniya watau Aleister Crowley.

Ku kasance tare da mu don ci gaban wannan labari


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN