Isyaku Garba | Birnin kebbi | 25-6-2018
A yau Litinin 25-6-2018 aka saurari shigar da kara da hukumar EFCC ta yi a kan tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari tare da wasu mutum uku, Sunday Dogonyaro, Abdullahi Yelwa tare da wani tsohon Akanta Janar na jihar Kebbi a zamanin mulkin Sa'idu Dakingari a kan aikata ba daidai ba da ya shafi miliyoyin kudi a babban Kotun tarayya da ke garin Birnin kebbi karkashin jagorancin mai shari'a Justice Simon Amobeda.
Da misalin karfe 10:00 na safiyar yau ne aka saurari jawaban Lauyoyin EFCC da na wadanda ake kara. Lauyan Sai'idu Dakingari ya gabatar da kudurin cewa Lauyoyin Gwamnati basu bi ka'idar doka wajen gabatar da takardar kara ga waanda yake karewa ba, amma a nashi zartarwa a kan zancen, Alkalin Kotun ya karanto sashe na doka da ya ba Kotun hurumin ci gaba da sauraron shari'ar.
Sakamakon haka, Lauyan Gwamnati ya bukaci Kotu ta bayar da izinin kamo tsohon Gwamnan domin ya gurfana a gabanta. Lauyan na mai kafa hujja ta hanyar karanto ayoyi da sashe na doka da ya bukaci ayi haka.
Amma a nashi bayani, Lauyan Sa'idu Dakingari ya roki Kotu cewa kada ta sa a kama Dakingarai tare da wadanda basu zo ba a zaman Kotun na yau, amma ya roki Kotu ta basu dama domin ganin cewa wadanda ake zargin sun halarci zaman Kotu na gaba da kansu.
Tun farko dai, Lauyan Sa'idu Dakingari ya yi jayayya a kan wa'adin kwana bakwai da ya kamata a ba wanda yake karewa domin ya shirya, amma Lauyan Gwamnati ya karanto sashe na doka da ya yi muhawwara a kan haka.
Daga bisani dai Alkalin Kotu ya ce Kotu ta gamsu da cewa an sanar da Sa'idu Dakingari cewa EFCC ta yi kararsa a madadin Gwamnatin tarayya, kuma Kotu ta gamsu da cewa an bi matakai da suka dace wajen sanar da Dakingari cewa Kotu tana neman shi.
Haka zalika, Alkalin ya ki amincewa da rokon da Lauyan Gwamnati ya yi ma Kotu cewa Kotu ta bayar da umarni domin a kama Dakingari, yana mai cewa domin ganin an yi adalci ga kowane bangare, Kotu ta aminta da bukatar wanda ake karewa cewa a yi masu lamuni har ranar 2 ga watan Yuli lokacin zaman Kotu na gaba domin wadanda aka yi kara su zo Kotun da kansu.
Alkalin ya yi gargadin cewa matukar wadanda ake kara basu bayyana ba a Kotu ranar 2 ga watan Yuli, lallai wannan zai sa Kotu ta yi amfani da sashen doka da ya bata dama ta bayar da izini domin a kamo wadanda aka yi kara domin su gurfana a gaban ta.
Daga karshe Justice Simon Amobeda ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 2 ga watan Yuni 2018 domin ci gaba da gudanar da shari'ar
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
ZIYARCI SENIORA TECH DOMIN FLASHING KO CIRE SECURITY NA WAYAR SALULARKA A GARIN BIRNIN KEBBI. SHAGO MAI LAMBA 50, HAWA NA SAMA DAGA GEFEN HAGU, YAMMA DA GIDAN MARIGAYI WAZIRI UMARU. TAUSHI PLAZA, TITIN AHMADU BELLO
A yau Litinin 25-6-2018 aka saurari shigar da kara da hukumar EFCC ta yi a kan tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari tare da wasu mutum uku, Sunday Dogonyaro, Abdullahi Yelwa tare da wani tsohon Akanta Janar na jihar Kebbi a zamanin mulkin Sa'idu Dakingari a kan aikata ba daidai ba da ya shafi miliyoyin kudi a babban Kotun tarayya da ke garin Birnin kebbi karkashin jagorancin mai shari'a Justice Simon Amobeda.
Da misalin karfe 10:00 na safiyar yau ne aka saurari jawaban Lauyoyin EFCC da na wadanda ake kara. Lauyan Sai'idu Dakingari ya gabatar da kudurin cewa Lauyoyin Gwamnati basu bi ka'idar doka wajen gabatar da takardar kara ga waanda yake karewa ba, amma a nashi zartarwa a kan zancen, Alkalin Kotun ya karanto sashe na doka da ya ba Kotun hurumin ci gaba da sauraron shari'ar.
Sakamakon haka, Lauyan Gwamnati ya bukaci Kotu ta bayar da izinin kamo tsohon Gwamnan domin ya gurfana a gabanta. Lauyan na mai kafa hujja ta hanyar karanto ayoyi da sashe na doka da ya bukaci ayi haka.
Amma a nashi bayani, Lauyan Sa'idu Dakingari ya roki Kotu cewa kada ta sa a kama Dakingarai tare da wadanda basu zo ba a zaman Kotun na yau, amma ya roki Kotu ta basu dama domin ganin cewa wadanda ake zargin sun halarci zaman Kotu na gaba da kansu.
Tun farko dai, Lauyan Sa'idu Dakingari ya yi jayayya a kan wa'adin kwana bakwai da ya kamata a ba wanda yake karewa domin ya shirya, amma Lauyan Gwamnati ya karanto sashe na doka da ya yi muhawwara a kan haka.
Daga bisani dai Alkalin Kotu ya ce Kotu ta gamsu da cewa an sanar da Sa'idu Dakingari cewa EFCC ta yi kararsa a madadin Gwamnatin tarayya, kuma Kotu ta gamsu da cewa an bi matakai da suka dace wajen sanar da Dakingari cewa Kotu tana neman shi.
Lauyoyin Gwamnati |
Layyin Sa'idu Dakingari |
Lauyan wadanda aka yi kara |