• Labaran yau


  Budurwa ta sha dukar kawo wuka kan zargin yin zina a watan Ramadan

  A Morocco wasu gungun matasa sun lakada wa wata daliba mai kimanin shekaru 20 da haifuwa duka da kulakai,sakamakon tuhumar ta da suke da yin zina a watan Ramadan.

  A yanzu haka bidiyon wannan lamarin ya gama duniya,inda kowa ke ci gaba da fadar albarkacin bakinsa.

  Bidiyon na nuna fuskokin wasu fusatattun matasa wadanda suka far wata matashiya wacce ke zaune da wani tsoho a wata mota.

  Matashiyar ta yi kokarin fada musu cewa, ita daliba ce,kuma tsohon da ke tare da ita, direba ne.

  Amma ba su bar ta karasa ba,inda nan take suka far ma ta,yayin da jama'ar unguwa kuma, suka mara musu baya ta hanyar jifar yarinyar,suna cewa

  "Zina a wata mai tsarki, ba ki ji kunya ba".

  Wannan lamarin yayi matukar tayar da hankalin al'umar ciki da wajen kasar Morocco.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com 

  #TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Budurwa ta sha dukar kawo wuka kan zargin yin zina a watan Ramadan Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama