Sakataren
janar na NATO, Stoltenberg ya sanar da cewa ba zasu taimaka wa
Isra'ila,idan har maki babbar makiyiyarta,wato Iran ta kai ma ta
farmaki.
Stoltenberg ya furta wannan kalamin gaban manema labarai kafar Associated Press (AP).
Haka zalika a ranar Asabar din ma,Stoltenberg ya maimata wannan furucin a jaridar Der Speigel ta kasar Jamus,inda ya ce,
"Isra'ila
kawa ce ba mambar NATO ba.Babu wani tilashin bai Isra'ila kariya kamar
sauran kasashe.Kamata yayi mu nesanta kanmu daga duk wata matsalar da
za ta gurgunta yunkurin samar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma
guje wa haddasa fitintinu a Gabas ta tsakiya"
Wannan jawabin na sakataren janar na NATO ya zo daidai lokacin da Iran da Isra'ila ke ci gaba wasa wukake da harar juna.
Firaministan
Isra'ila Benyamin Netanyahu ya soki yarjejeniyar nukiliyar da wasu
kasashen Yamma suka kulla da shugabannin kasar Farisa.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI