Manyan 'yan wasan da ba za su tafi gasar cin kofin duniya ba
Isyaku GarbaJune 03, 2018
0
Manyan 'yan wasa da dama ne kasashensu za su buga gasar cin kofin duniya a Rasha ba tare da su ba.
Wasu
daga cikin 'yan wasan, raunin da suka ji ne ya hana su zuwa gasar,
yayin da wasu kuma aka ki gayyatarsu daga cikin 'yan wasan da za su buga
gasar a Rasha. Kasashe 32 ne za su buga gasar da za a fara a ranar 14 ga watan Yuni. BBC ta yi nazari game da wasu daga cikin manyan 'yan wasan da za su kalli wasan a gida duk da kasashensu na fafatawa a gasar.
Cesc Fabregas
Dan wasan tsakiya na Chelsea Cesc Fabregas na cikin
'yan wasan da kocin Spain Julen Lopetegui ya ki gayyata domin buga gasar
cin kofin duniya a Rasha.Fabregas na cikin tawagar Spain da suka lashe kofin duniya da aka gudanar a Afirka ta kudu a 2010. Tsohon dan wasan na Arsenal da Barcelona ya wakilci Spain a gasar cin kofin duniya sau uku, a shekarar 2006 da 2010 da 2014.
Alvaro Morata
Alvaro Morata ba ya cikin jerin 'yan wasan Spain 23 da za su buga gasar cin kofin duniya a Rasha.Dan wasan mai shekaru 25 ya ci kwallaye 11 a kakarsa ta farko a Chelsea. Kocin Spain ya zabi Diego Costa ne a madadin Alvaro Morata a matsayin lamba 9 a tawagar kungiyar.
Dani Alves
Raunin da Dani Alves ya samu a guiwarsa ne ya hana shi zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha.Dan
wasan na Paris Saint Germain yana cikin manyan 'yan wasan Brazil da
suka taimakawa kasar zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha. Amma dan wasan zai kauracewa gasar saboda raunin da ya samu a wasan karshe da ya buga wa PSG na lashe kofin Faransa.
Anthony Matial
Dan wasan na Manchester United ba ya cikin 'yan wasan da za su buga wa Faransa gasar cin kofin duniya a Rasha.Ko da yake Martial yana cikin 'yan wasan da ke jiran tsammanin ko za a gayyace su zuwa gasar. Martial, mai shekara 22, ya fuskanci kalubale a bana a United, inda tun watan Janairu bai sake zura kwallo a raga ba.
Juan Mata
Mata ba ya cikin 'yan wasan da za su buga wa Spain gasar cin kofin duniya a Rasha.Dan wasan na Manchester United yana cikin 'yan wasan da suka taimakawa Spain lashe kofin duniya a Afirka ta kudu. Amma a bana ba ya cikin zabin kocin Spain.
Alexandre Lacazette
Lacazette da ke taka leda a Arsenal na cikin manyan 'yan wasan Faransa da kocin kasar Didier Deschampsya ajiye.Dan wasan ya ci wa Arsenal kwallaye 19 a dukkanins wasannin da ya buga wa kungiyar a kakar da aka kammala. Baya ga Lacazette, Dechamps ya kuma ajiye Kingsley Coman da Adrien Rabiot da Anthony Martial, dukkaninsu 'yan wasan gaba. Kocin ya tafi da Antoine Griezmann da Olivier Giroud da Kylian Mbappe da Ousman Dembele.
Jack Wilshere
Jack wilshere na cikin 'yan wasan da Kocin Ingila Southgate ya ajiye.Dan
wasan na Arsenal ya yi mamakin rashin gayyatarsa zuwa gasar cin kofin
duniya a Rasha duk da ya buga wa Ingila wasan sada zumunci a watan
Maris.
Joe Hart
Golan na Ingila ba ya cikin 'yan wasan da za su wakilci Ingila a gasar cin kofin duniya.Kocin Ingila Southgate ya zabi Nick Pope golan Burnley maimakon Joe Hart da ke tsaron ragar West Ham United. Hart ya fuskanci kalubale a matsayin golan Ingila tun lokacin da Manchester City ta rabu da shi a matsayin golanta.
Karim Benzema
Benzema yana cikin 'yan wasan da suka kafa tarihi a Real Madrid bayan sun lashe kofin zakarun Turai sau uku a jere.Amma dan wasan ba ya cikin tawagar Faransa da za su haska a gasar cin kofin duniya. Ana ganin dai sabanin da ke tsakanin dan wasan da kocin kasar ne ya yi tasiri ga rashin gayyatarsa.
Dimitri Payet
Payet na cikin 'yan wasan da za su kalli gasar cin kofin duniya a gida saboda raunin da yake fama da shi.Dan
wasan na Faransa ya ji rauni ne a wasan karshe na Europa League da
kungiyarsa Marseille ta sha kashi a hannun Atletico Madrid. Payet ya taka rawar gani a gasar cin kofin Turai da aka gudanar a Faransa a 2016. Dan wasan tsakiyar ya ci kwallaye 10 a raga a bana.
Mauro Icardi
Mauro Icardi yana cikin manyan 'yan wasan da za su
kalli gasar cin kofin duniya a gida bayan rashin gayyatarsa a tawagar
Argentina.Kocin Argentina Jorge Sampoali ya ki gayyatar dan wasan na Inter Milan duk ya ci kwallaye 29 a kakar bana. Kocin ya zabi Paulo Dybala da Aguero da Higuan da Messi a madadin dan wasan. Alex Oxlade-Chamberlain Raunin da Oxlade-Chamberlain ya ji ne ya hana ma sa zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha.Dan wasan na Ingila ya ji rauni ne a fafatawar Liverpool da Roma a gasar cin kofin zakarun Turai wasan dab da karshe a Anfield.
Dani Carvajal
Carvajal ya ji rauni gasar Zakarun Turai wasan karshe da aka fafata tsakanin Real Madrid da Liverpool.Raunin da dan wasan ya ji ne ya haramta ma shi wakiltar Spain a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Pedro
Pedro na cikin 'yan wasan da kocin Spain ya ajiye daga cikin tawagar da za su buga wa kasar gasar cin kofin duniya.
Pedro da ke taka leda a Chelsea ya ci kwallo bakwai a dukkanin wasannin da ya buga a bana. Tsohon
dan wasan na Barcelona ya wakilci Spain a gasar cin kofin duniya sau
biyu, ciki har da 2010 da kasar ta lashe kofin gasar. #BBC
Seniora Tech tana N0.50 Taushi Plaza, Bello way Birnin kebbi. Ita ke tafiyar da shafukan isyaku.com da Seniora News a karkashin kampanin Seniora Int'l Ltd RC 1470216
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI