Lauyan Shugaban Amurka ya ce
watakila Shugaban na da ikon yi wa kansa afuwa idan har a ka kama shi da
wasu laifuka a binciken da a ke yi na sa hannun Rasha a zaben shugaban
kasar na shekarar 2016.
Ya kuma ce Shugaba Trump ba zai yi wa kansa afuwa ba domin hankali ba zai dauka ba kuma hakan na iya sa wa a tsige shi.
Haka kuma, Mr Giuliani ya ce babu tabbas a kan ko Mr Trump zai amince a tattauna da shi, a wani fanni na binciken da Lauya na musamman Robert Mueller ke yi.
Sai dai da alama, lauyoyin Shugaban za su hana shi bayar da shaida.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
BBC
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI