• Labaran yau


  Yadda yaki tsakanin kungiyoyin asiri 2 ke cin rayukan mutane a Calabar

  Tun makonni da suka gabata aka fara samun damuwa sakamakon yadda yaki tsakanin wasu kungiyoyin asiri guda biyu a karamar hukumar Calabar ta kudu yake cin rayukan 'yan kungiyoyin, domin da sanyin safiyar Litinin an sami gawar wani 'dan kungiyar asiri da aka kashe kuma aka gundule hannunsa a unguwar Wilkie kusa da White House a cikin birnin Calabar.

  Kwanakin baya dai mutun hudu sun rasa rayukansu tsakanin kungiyoyin asiri na Balack axe da Vikings wadanda ke matukar gaba na ikon mallakar birnin Calabar sakamakon haka suke farautar 'ya'yan kungiyoyin juna suna kashewa da rana tsaka.

  Hukumar 'yansanda na jihar Cross Rivers tana hubbasa domin ganin ta faruci tare da kama 'ya'yan kungiyoyin asirin.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda yaki tsakanin kungiyoyin asiri 2 ke cin rayukan mutane a Calabar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama