• Labaran yau


  Shakira ta watsa wa Isra'ila kasa a ido don goya wa Falasdinu baya

  Shahararriyar mawakiyar kasar Colombia,Shakira ta watsa wa Yahudawan Isra'ila katsa ido don nuna goyon bayanta ga Falasdinawa.

  Shakira ta fasa yin shagalin da ta shirya yi a Tel Aviv, babban birnin kasar Isra'ila,a ranar 9 ga watan Yulin bana, don yin Allah wadai da kisan Falasdinawa.

  Kungiyoyin masu fafutukar share kwallan Falasdinawa da dama, sun aika wa mashahuriyar mawakiyar goron gayyata don kakaba wa Isra'ila takunkumi a fannin ilimi da raya al'adu,inda tuni ta yi maraba da yunkurinsu.

  Shakira wacce ta lashe lambar yabo ta Grammy,kana jakadar asusun kula da kananan yara na Majalisar ta Dinkin Duniya, UNICEF,ta sanar da cewa,ta fasa yin shagalin da ta shirya yi a Isra'ila,don yin Allah wadai da kisan gillar da kasar Yahudu take ci gaba da yi wa al'umar Falasdinu.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  #TRT 
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shakira ta watsa wa Isra'ila kasa a ido don goya wa Falasdinu baya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama