Dutsen Merapi da ke tsibirin Java na Kasar Indonesiya ya yi bindiga tare da fara aman wuta.
Sanarwar
da aka fitar daga cibiyar nazarin kan duwatsu masu aman wuta da yanayin
kasa (PVMBG) ta ce, hayaki da tartsatsin wutar da dutsen Merapi ya ke
fitarwa a garin Yogyakarta ya kai nisan kilomita 6 a sama.
Kakakin
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (BNPB) Sutopo Purwo Nugroho kuma cewa
ya yi hayaki da harshen wutar da dutsen ke fitarwa ba su janyo dakatar
da zirga-z,rgar jirage a filin tashi da saukar jiragen sama da ke garin
Adisutjipto.
Nugroho ya yi gargadi kan a kwashe jama'ar da nisan kilomita 3 daga inda dutsen ya ke.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT