1) Cin soyayun abubuwa Mutum ya takaita ciye-ciyen soyayun abubuwa musamman masu maiko sosai da kuma cin duk wani abinci mai dauke da sinadarin acid misali lemun tsami, lemun taba, lemu da innabi da tumatur da makamantansu.
2) Cin abinci mai dauke da yaji da abincin gwangwani Abinci mai yaji sosai ko kuma abincin gwangwani suna dauke da sinadarai wanda aka sanya don su hana abincin baci da wuri sai dai kuma wannann sinadarin na kara sanya sinadarin acid na cikin dan adam ya karu.
3) Takaita amfani da suga Masana sun shawarci masu ciwon ulcer su guji amfani da abinci masu dauke da siga sosai musamman abincin gwangwani da ake sarafawa a kamfanoni.
4) Mugun ci yayin sahur ko bude-baki (iftar) da kuma jinkirta bude-baki Ana bukatar duk mai fama da ciwon ulcer ya guji cika cikinsa tatul yayin sahur ko bude- baki iftar, kana ba’a son mutum ya jinkirta cin abinci bayan an sha ruwa saboda sinadaren acid da ke cikinsa su samu abincin da za suyi aiki dashi.
5) Gujewa shan taban cigari Shan taban cigari yana da iloli da yawa ga dan adam da suka shafi huhu da wasu tsokokin jiki, har ila yau, shan tabar na sanya sinadarin acid din cikin dan adam yayi yawa kuma tabar na hana warwakewar raunin da mai ulcer ke dashi a hanjin sa
6) Guji magunguna ciwon jiki musamman ba tare da izinin likita ba Mafi yawancin magungunan ciwon jiki da ake amfani da su suna cikin wata rukunnin magunguna ne da ake kira turence ‘NSAIDS’ wanda suna dauke da sinadarin da ke yiwa fatar ciki ko hanjin dan adam illa, saboda haka duk wanda kai azumi ya kamata ya tambaya likitansa ko masana kimiyyan magunguna kafin yayi amfani da magunguna ciwon jiki musamman lokacin azumi.
Abubuwan da masu ciwon ulcer ya dace su ci 1) Mai fama da ciwon ulcer ya kamata ya karkata ne zuwa ga cin abincin da jikin dan adam ke sarrafa su a hankali misali doya, hatsin da ba’a surfe ba, gyda, wake, waken soya, kubewa, cabeji da sauransu.
2) Kayan itatuwa kumar da dabino, ayaba, yalo da sauransu.
3) A komawa gashashen nama a maimakon soyaye 4) Idan kuma likitoci sun rubuwata mutum magunguna, sai ya rika sha lokutan da suka umurce shi da sha galibi lokutan sahur ko iftar.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Madogara: Hausa.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI