• Labaran yau


  Karya ta kare bori ya kashe boka, EFCC ta yi karar Sa'idu Dakingari kan badakalar N700m a Kebbi

  Da tsakiyar ranar Laraba misalin karfe 1:51 na rana an mika ma wani ma'aikacin gidan tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari takardar kara da hukumar EFCC ta shigar a wata babban Kotun tarayya da ke garin Birnin kebbi.

  Wata majiy ta ce an sha yin hannun makafi da tsohon Gwamnan yayin da yunkuri na a bashi takardar kara da ake yi masa ya ci tura har tsawon wata daya.

  Amma daga karshe dai an mika takardar karar ga wani ma'aikacin gidansa da ke GRA Birnin kebbi domin ya mika takardar ga ubangidansa Dakingari.

  Hukumar EFCC ta yi karar Sa'idu Dakingari a kan laifuka 15 da take tuhumarsa na aikata ba daidai ba tare da karbar Naira miliyan dari bakwai (N700.000.000) daga tsohuwar Ministan albarkatun man fetur Diezani Allison Madueke.

  Sa'idu Dakingari na fuskantar tuhuma ne tare da wasu mutum uku.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karya ta kare bori ya kashe boka, EFCC ta yi karar Sa'idu Dakingari kan badakalar N700m a Kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama