• Labaran yau


  Yan sanda sun damke yan Shi’a 42 masu alaka da kisan dan sanda a Kaduna


  Hukumar yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta damke mambobin kungiyar Shi’a 42 tattare da kisan wani jami’in dan sanda a jiya Alhamis, 21 ga watan Yuni a jihar Kaduna. 

  Kakakin hukumar yan sanda, Mukhtar Aliyu, ya bayyana wannan kamu ne a yau Juma’a, 22 ga watan Yuni a jihar Kaduna. Ya ce lallai za’a gurfanar da wadannan mutane 42 muddin an kammala bincike a kan su. Damke wadannan yan Shi’a ya faru ne bayan rikici ya barke tsakanin jami’an yan sanda da yan kungiyar Shi’a masu zanga-zangar cigaba da tsare shugabansu kuma malaminsu, Sheik Ibrahim Zakzaky 

  NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa an hallaka dan sanda daya har lahira a sabuwar rikici da ya barke tsakanin yan sanda da yan kungiyar Shi'a a zanga-zangan da sukeyi kan cigaba da tsare shugabansu, Sheik Ibrahim Zakzaky. Kakakin hukumar yan sanda a jihar Kaduna, Muktar Aliyu, ya tabbatar da wannan labari da ya faru a yau Alhamis, 1 ga watan Yuni 2018. 

  Game da cewarsa, dan sandan na tafiyarsa a kan hanya kawai sai yyan Shi'an sukayi masa ribiti da caccaka masa wuka har lahira. Sheikh Ibrahim El-Zakzaky dai yana gurfana a kotu ne kan laifin tara mabiya ba bisa doka ba, kokarin fito-na-fito da gwamnati.
   

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yan sanda sun damke yan Shi’a 42 masu alaka da kisan dan sanda a Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama