Bidiyo: Yadda Jokolo ya caccaki gwamna Bagudu - ISYAKU.COM
June 02, 2018
0
Sarkin Gwandu na 19 Alh. Al-Mustapha Jokolo, ya ce duk da umurni da Kotu ta bayar a biya shi albashinsa da alawus-alawus nasa na tsawon shekara, 10 amma gwamnatin jihar Kebbi bata biya shi ba, sakamakon haka ya gabatar da koke ga hukumomin da lamarin ya shafa amma har ila yau ba a aiwatar da umurnin Kotun ba.
Ya kara da cewa gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi zai gurfana a Kotun koli ranar 5 ga watan Yuli bisa tuhumar aikata ba daidai ba.
Haka zalika, Jokolo ,a faifen bidiyon ya mance da sunan gwamnan jihar Kebbi sai da wani hadiminsa ya tuna mashi, bayan an ga Basaraken yana daka ma hadiminsa tsawa cewa "shut up" watau "yi shiru".
Daga Isyaku Garba
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI