Shahararriyar jarumar nan ta dandalin Kannywood, da
tauraruwarta ke kan haskawa, Umma Shehu, ta shirya saka kafar wando daya da mai
yi mata bita da kulli a masana'antar fim.
Ko da yake jarumar bata bayyana sunan wanda take caccaka ba,
jarumar ta bayyana cewa baza ta damu ba idan har aka kore ta daga masana’antar.
A sakon da ta wallafa a shafin ta na kafar sada zumunta, Umma bata boye irin
rashin mutunci da zata iya yi ga duk mutumin da ya tokale ta ba.
Tana mai cewa "Na fika rashin mutunci kuma ni da kake
kallo bana tsoron kowa sai Allah".
Ga cikakken sakon da ta fitar kamar
haka; "Babu abunda ya dame ni da kai idan ka ga dama kasa a kore ni a
kannywood dan nasan bakai ne me bada daukaka ba Allah ne dan haka wallahi na fi
ka rashin mutunci ni da kake kallona ba na tsoran kowa sai Allah ni ummah Shehu
nafi karfin na baka hakuri ba tare da na maka laifi ba dan kasa anyi casting
dina sai me ka manta da Allah shine meyi kafin kaima kanka ai am maka dan haka
ba cire ni ya kamata ayi ba korana ya kamata kayi nonsense ni ba zansa hoto ina
fadanci ba don babu abunda nake nema agun kowa sai gun Allah kaje ka tambayi
waye ummah shehu za’a gaya maka irin rashin mutuncin da zanyi kuma idan ka
tashi tambaya kazo unguwarmu ka tambaya anan ne zaka ji ainihin halin ummah
babu wanda ya isah naime fadanci idan ina sonka Ina sonka idan bana sonka bana
sonka ni haka nake dan haka to hell with you".
Idan ba'a manta ba a kwanakin baya, Ummah Shehu, ta jawo
tsegumi a kafafen sada zumunta bisa ga tambayoyi da mai gabatar da shiri yayi
mata hirar ta da telebijin na Arewa24 a cikin wani shiri na musamman. Bayan
hirar dai jarumar ta fito fili ta bayyana cewa bata ji haushin abun da ya faru
tsakaninta da mai gabatarwa ba.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng
Tags:
LABARI