• Labaran yau


  Chakwakiya, kasar Canada za ta halalta shan tabar wiwi a fadin kasar

  Nan ba da dadewa ba kasar Canada za ta halalta shan tabar wiwi a fadin kasar bayan majalisar Dattawar kasar ta kada kuri'ar amincewa da kudurin dokar mayar da shan tabar ta wiwi halal a kasar.

  Yan majalisar Dattawar sun kada kuri'a 52-29 ranar Talata wanda hakan ya bayar da rinjaye ga wadanda suka aminta da dokar'.

  Kasar Canada ita ce ta biyu a fadin Duniya da za ta halalta shan tabar wiwi a fadin kasar bayan kasar Uraguay da ta halalta noma tare da shan tabar wiwi a 2013.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Chakwakiya, kasar Canada za ta halalta shan tabar wiwi a fadin kasar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama