Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun da
ke kudancin Najeriya ta tabattar da mutuwar wani magidanci da matarsa da
kuma 'ya'yansa uku bayan sun tare a sabon gidansu da ke garin Sagamu.
Sai dai rahotanni sun ce ana kyautata zaton feshin wani maganin da aka yi ne a sabon gidan ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
Wani na kusa da iyalan ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Najeriya (NAN) cewa sun rika jin wari sosai bayan kwana daya da iyalan suka shiga sabon gidan
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
BBC
Tags:
LABARI