A ranar Alhamis, 7 ga
watan Yuni, majalisar dattawa ta yi watsi da June 12 a matsayin ranar
kaddamar da sabbin jami’an gwamnati. Read more: https://hausa.naija.ng/1173987-yanzu-yanzu-majalisar-dattawa-ta-ki-amincewa-da-12-ga-watan-yuni-a-matsayin-ranar-rantsar-da-sabbin-jami-gwamnati.html#1173987
A ranar Alhamis, 7 ga watan Yuni, majalisar dattawa ta yi
watsi da June 12 a matsayin ranar kaddamar da sabbin jami’an gwamnati.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
sanar a shafinsa na Facebook cewa June 12 zai koma ranar damokradiyya.
Majalisar masu rinjayen tace lallai ranar 29 ga watan Mayu shine ranar rantsar
da sabbin jami’an kasar
Yan majalisan sun kuma bayyana bukatar biyan dukkanin
kudaden albashi da alawus alawus din manyan jami’an da aka zaba a waccan
lokacin ga iyalansu.
A halin da ake ciki, mataimakin shugaban majalisar dattawa,
Ike Ekweremadu ya bayyana cewa akwai bukatar gyara kundin tsarin mulki idan har
12 ga watan Yuni ya koma ranar Demokradiyya.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI