Madigo: Dalilai da ya sa mata ke neman 'yan uwansu mata, illoli da matakan kariya

Madigo wata hanya ce da Mace zata biya bukatar ta ga yar uwarta Mace, ta hanyar sunbatar juna, shafe-shafe, rungume-rungume, da duk wani abun da zai  kwantar masu da sha’awar su ko kuma ya gamsar da su. Mafi yawan Matan da ke wannan sana’ar suna afkawa wannan ibtila’in ne a sanadiyar kawance da masu irin wannan dabi’on, wasun su kan fada ne a sanadiyar kwadayin abin duniya, wasu rashin yin Aure da sauran su.


Wata yar Madigo da nayi hira da ita, ta shaida min dalilin tana afkawa wannan harkan. Ta ce “Maigidana ya kasance mutun ne mai son kai, ba ya  damu da biyan bukata taba, daya samu biyan tasa bukatar”. Ta ci gaba da cewa “Mu na zaune ahakan har zuwa lokacin da na nemi ya sake ni. Bayan mun rabo na hadu da wata da muka kulla kawance, har ta kai ta tare a gidana, daga nan muka fara biyawa junan mu bukata. Da na tambaye ta ko zata koma wa uban yayanta? Sai tace “Hmmmm! Ba  zaki gane ba, wallahi san yanzu bana sha’awar Namiji”.

ALAMOMIN MASU MADIGO



1. Zaki ga mafi yawan masu wannan dabi’ar suna saka sarka a kafar su. Ba lallai bane duk wanda ya sa sarka a kafa ya kasance dan madigo, wasu kan sa ne saboda suna da ra’ayin hakan


2. Mace ta yawaita yabon kyawon fuskar ki da na diran jikin ki. Yar uwa ki kiyaye duk macen da takan yawaita yabon dirar jikin ki ko kyan fuskar ki, to akwai ayar tambaya gane da ita
3. Sanya zobe a yatsun kafa tabi’a ceta masu yin madigo, ta hanyar wannan alama ce za su gane junan su. Akan samu wasu matan da ke da ra’ayin sanya zoben ba tare da sanin aibin sanyawar ba.
4. Za kiga mace tana da kawaye mata da suke yawan  ziyarta ta ko kuma ita tana yawan zuwa wurin su, ana shegewa dakin ana shewa da tabe-tabe. Yar uwa ki guje shiga cikin irin wayan nan kawayen.
5. Yar uwa ki guje kawar da bata jin kunyar sakin al’aurarta a gabanki, ko kuma mai yawan kalle-kalle fina-fina na batsa ko kuma na yan madigo.
6. Ki guje kawar da take yawan kai maki runguma, ko ta rika kallun kirjin ki a lokacin da kika yi kuskuren sakin wani sashe na tsiraicin ki.

ILLOLIN YIN MADIGO

Madigo yana daya daga cikin manyan laifukan da Ubangiji ya kyamata, sai dai shari’ah bata bada ainihin wani hukuncin da za’ayi wa masu madigo. Sai dai mafi yawan malamai suna ganin za’ayi masu hukunci dai-dai da na yan luwadi.


1. Akan iya daukar cutukan zamani ta hanyar madigo.
2. Yin madigo yana raunana imanin mutum
3. Yana gusar da kunya gaba daya
4. Fushin Allah ga masu wannan aikin
5. Gushewar mutunci a idon mutanen kirki
6. Masu yin wannan aiki sukan samu kansu a cikin kuncin rayuwa
7. Rashin yin kyakkyawan karshe ga masu aikata madigomadigo
8. Rashin sha’awar Aure
9. Za a kai lokacin da mace bata sha’awar namiji gaba daya




HANYOYIN BARIN MADIGO

Wajabi ne ga duk masu irin wannan dabiar ta madigo da suji tsoron Allah su nisantar da kan su ga barin yinsa. Su tuna ko wane lokaci za su iya riskar mahaliccin su bayan suna aika wannan mummunar aikin. Yar uwa ga kadan daga cikin hanyar da zaki bi ki nisanci kanki da wannan dabi’on.

1.  Ki tuba da niyar ba zaki sake aikata wannan aikin ba

2.  Ki nisantar da kanki ga duk wata kawa da kuke wannan harkan

3.  ki yaawaita istigifari

4. A duk lokacin da sha’awar yin hakan ya taso maki, ki yi alwala ki karanta daga abinda ya  sauwaka na daga Qur’ani.

5. Nisanta kan ki ga kallun fina-finan  da hoto nan batsa

6. ki rika sawa ranki azabar da ke cikin yin maddigo, a duk lokacin da sha’awar yin hakan ya   ta so maki

7. ki yawaita yin azumin Litinin da Alhamis

8. ki tuna kusancin Ajalinki, kwanciyar kabari, hisabi da kuma makomar masu irin laifin ki.

Ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa da ka kiyaye mu da fadawa cikin wannan halin, ka shiryar da masu yi, ka gafarta mana ka kuma anshi tuban mu.

Ina mai farin cikin samun comment dinku game da shawarwari, illoli, da alamun da za agane masu wannan harkan wanda ban kawo ba.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY .Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com .Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira.

ciwonyamace, tare da godiya ga meelablog.

ZIYARCI SENIORA TECH DOMIN FLASHING KO CIRE SECURITY NA WAYAR SALULARKA A GARIN BIRNIN KEBBI. SHAGO MAI LAMBA 50, HAWA NA SAMA DAGA GEFEN HAGU, YAMMA DA GIDAN MARIGAYI WAZIRI UMARU. TAUSHI PLAZA, TITIN AHMADU BELLO.



Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN