• Labaran yau


  Karanta abin da Gwamna Bagudu ya ce kan social media da amfani da wayar salula

  Daga Isyaku Garba- Birnin kebbi
  Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya kalubalanci ma'abuta amfani da kafar sada zumunta na Social Media tare da al'ummar jihar Kebbi su kasance masu zakulo tsare-tsare da hanyoyi da za a iya amfani da wayar salula domin cin amfanin kimiyyar zamani bisa la'akari da ci gaban Duniya ta fannen kimiyyar wayar salula.

  Gwamna Bagudu ya yi wannan jawabi ne ranar 25 ga watan Ramadana watau 10/6/2018 a gidan Gwamnatin jihar Kebbi, bayan budin bakin Azumi tare da fiye da 'yan Social Media 90 da suka halara daga dukannin kananan hukumomin jihar Kebbi guda 21.

  Bagudu ya yi bayani a kan amfanin aiki da hankali tare da natsuwa, nazari da tantancewa kafin a wallafa labari a kowace kafar sadarwa.

  Kalli cikakken jawabin Gwamna Atiku Bagudu:


  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta abin da Gwamna Bagudu ya ce kan social media da amfani da wayar salula Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama