Wata kotu a Najeriya ta daure Tsohon
Gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 16 a gidan yari bayan ta same shi
da laifin cin amana da almubazzaranci.
Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017.
Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da wata kotu ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.
An yanke masa shekara 14 saboda cin amanar duniyar jama'a, sannan shekara biyu saboda almubazzaranci.
Za a hade hukuncin wuri guda, wanda hakan ke nufin zai yi zaman jarum na shekara 14.
Mr Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke unguwar Gudu.
Mai shari'a Bamijoko ta ce Sanata Dariye ya barnatar da sama da naira biliyan daya da aka bai wa jihar domin shawo kan matsalar zaizayar kasa.
Lauyansa Kanu Agabi ya soki sahihancin shaidun da aka yi amfani da su wurin samunsa da laifi, amma mai shari'ar ta ce shaidun sun tabbatar da almundahanar da aka tuhume shi da aikatawa.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
BBC
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI