Bincike ya nuna cewa Hantar É—an Adam tana aiki daban-daban
sama da 500 domin dai gangar jiki ta zauna lafiya
Amma idan hantar mutum ta fara samun matsala, wasu alamomi
irinsu tashin zuciya ko kwarnafi, amai da gudawa da kuma rashin É—anÉ—ano a baki
da sauransu ka iya bayyana. Idan bayan bayyanar waÉ—annan alamom mutum bai samu
kulawar da ta dace ba, manyan alamomi zasu biyu baya irinsu; matsala a tunani
(kwakwalwa) ruftawar dubura da kuma nason jini. Wasu lokutan idan abin yayi
tsanani mutum ka iya shiga cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwi koma ya sheka
barzahu.
1 - Sukari
Yawaitar shan suga na bawa haƙora matsala haka kuma ita ma
hanta bai barta a baya ba, domin yawaitar sukarin a jiki musamman wanda aka
sarrafa daga kamfani, yakan tattaro kibar da zata bawa hartar matsala. Bincike
ya nuna cewa irin wannan sukari kanyi kwatankwacin illar da giya take yiwa
hanta koda kuwa mutumin ba shi da kiba sosai ba.
A saboda haka ne masana suka shawarci mutane da su rage
ta’ammali da alawa mai mutukar zaki da cincin ko duk wani nau’in abinda aka
soya ko gasawa da fulawa mai sukari da yawa da kuma lemon kwalba masu zaki da
yawa.
2 - Kwaya ko maganin da suka maye gurbin sinadarin Vitamin A
Vitamin A na da mutukar muhimmanci ga jikin bin Adam, kuma
ana samunsa ne ta hanyar cin’ya’yan itatuwa masu kyau da ganyayyaki musamman
wadanda suke nau’in kalar ja ko kore da ruwan dorawa. Saboda cigaban zamani da
kuma rashin samun su Vitamin A ko kuma tsada da kayan marmari da na ganyayyakin
su keyi a wasu lokutan, sai aka samar da wasu magunguna na ruwa da kuma kwayoyi
da suke aiki a jiki kwatankwacinsu. Sai dai kuma yawaita shan irin wadannan
magunguna ka iya haifar da illa ga hanta, saboda haka kafin shansu sai a
tuntubi likita.
3 - Lemon kwalba
(Soft Drinks)
Bincike ya nuna cewa duk masu yawaita shan lemon kwalba suna
cikin hadarin kamuwa da kibar nan dake haifar da matsala ga hanta
(Non-alcoholic fatty liver disease (NAFLD). A shawarce shan kayan marmari ko
laimunan da aka yi su daga ‘ya’yan itatuwa shi ne ya fi ga lafiya dan Adam.
4 - Sarrafaffen Kitse (Trans Fats)
Wannan wani irin sinadari ne da kamfanunuwa kan sarrafa a
cikin abinci ko abin sha kamar bota (Butter), yawancinsu a hankali yake taruwa
kafin daga bisani yayi yawa a jiki, shi ma yakan haifar da matsala ga hanta a
kwana a tashi.
5 - Giya
Kamru uwar laifi shi ne kirarin da ake yi mata, baya ga
tumbele da gusar da hankali da take sawa dadin-dadawa tana muzgunawa wannan
sashin jiki mai muhimmanci wato hanta. Saboda aikin hanta ne ankewa da fitar da
duk datti da kuma guba, shan giya kan ninka mata aiki a sakamakon haka sai tayi
saurin gajiya karfinta ya kare domin duk ta karar da shi wajen kokarin wanke
dattin giyar.
6 - Sarrafaffen abinci (Fast food)
Dagaske ne kin bata lokaci don yin girki na da dadi musamman
idan mutum ba shi da isasshen lokaci, amma fa a kwana da sanin cewa, yawancin
irin wadannan abincin na dauke ne da sinadaren sanya kiba ko zakin da kan iya
bawa hanta matsala a kwana a tashi (calories da kuma fatty).
7 - Magunguna dangin Paracetamol (Acetaminophen)
Jin ciwon kai da ciwon baya ko wata ‘ya mashasshara ya sanya
mutane yawaita shan maganin Paracetamol ba tare da sanin irin illar da yake
yiwa jikinmu ba, yawaita shan irin wadannan magunguna na kashe gajiya ko ciwo
na illata hanta sosai. A don haka sai a tabbatar an duba ka’idojin shan sa ko
kuma a tambayi likita kafin amfani da shi.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng