APC ba addini bane don haka zan fita na bar ta da miyagu – Sanata Shehu Sani


Wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana jam’iyyar APC a matsayi hadakar miyagun mutane marasa gaskiya, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito. 

Shehu ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi a shirin kowani gauta na gidan rediyon Freedom, inda ya nuna bacin ransa da yadda ake tafiyar da jam’iyyar APC, wanda yace hakan akasin yadda aka gina tubalin jam’iyyar ne a tun farko. 

“An shirya za ayi adalci a jam’iyyar APC a baya, amma a yanzu an koma rashin gaskiya, abu biyu ne dama mutum ba zai iya rabuwa dasu ba, iyayenka ba zaka iya canzasu ba, haka ma addininka, don haka tunda dai jam’iyyar ba addini bace, zan fita daga cikinta. zamu sanar da inda zamu koma” Inji shi. 

Sanatan ya bayyana jam’iyyar APC a jihar Kaduna a matsayin mayaudariya, wanda ta gagara cika alkawurran da ta daukan ma al’ummar jihar:

 “Sun yi alkawarin daukan ma’aikata dubu goma sun buge da korar dubu hamsin, sun kasa yi ma jama’a ayyuka, sun yi alkawarin ingantaccen zabe sun buge da satar akwati.” Dangantaka dai ta yi tsami ne a tsakanin Shehu Sani da gwamnan jihar Kaduna tun bayan kammala zabukan shekarar 2015, inda Sanatan ke zargin gwamnan ya mayar da shi saniyar ware, shi kuma gwamnan ke zargin Sanatan na sunsunan kujerarsa don haka yake yi masa zagon kasa. 

Wannan rikici nasu ya kara ruruwa bayan da Sanatan yayi kutunkutun a matsayinsa na shugaban kwamitin ciyo bashi na majalisar dattawan Najeriya, ya hana gwamnatin jihar samun bashin dala miliyan 300 da babban bankin Duniya ta shirya bata.
 
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com 

hausa.naij.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN