• Labaran yau


  Jiragen yaki na sojin sama na Najeriya sun yi lugudin wuta a wasu kauyuka 3 a wata jiha ta tsakiyar Najeriya

  Jiragen saman yaki na sojin sama na Najeriya sun yi lugudin wuta a wasu garuruwa uku a cikin jihar Benue ranar Asabar. Daraktan hulda da jama'a na rundunar mayakan sama na Najeriya Air Vice Marshal Olatokumbo Adesanya ya shaida wa wakilin The Punch .

  Punch ta ce garuruwan da harin ya shafa su ne Katsina-Ala zuwa Zaki Biam har zuwa hanyar Wukari daga ciki har da kauyen Gbise,  Ayaka da kewaye.

  Rahoton ya kara da cewa yan kwanakin baya ne wasu matasa sanye da tufafin soji suka kai hari kan wani Janar na soji a kauyensu Maj. Gen. John Malu wanda ke kauyen Tse Adoor a mazabar Tiir a Tongov da ke karamar hukumar Katsina Ala na jihar ta Benue.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jiragen yaki na sojin sama na Najeriya sun yi lugudin wuta a wasu kauyuka 3 a wata jiha ta tsakiyar Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama