Abubuwan fashewa sun kashe a kalla
mutum 17 tare da jikkata wasu mutanen 80, tare da lalata wani masallaci a
babban birnin kasar Iraki, in ji majiyoyin lafiya.
Sai dai ta bayar da bayanin ainihin inda ma'ajiyar makaman take ba, amma wasu jami'an tsaro sun ce a cikin masallacin ne.
Magoyan bayan malamin Shi'ia Moqtada Sadr su ne suke amfani da masallacin
Mista Sadr ya jagoranci wani kawance na kishin kasa wanda ya hada da wasu kungiyoyin da ba na addini ba a zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi a watan jiya, inda ya ci 54 daga cikin kujeru 328.
Ya kuma jagoranci mayakan da suka yaki dakarun Amurka bayan sun far wa Iraki a shekarar 2003, amma a shekarun baya-bayan nan yana taimaka wa sojojin Irakin da Amurka ke mara wa baya a yakin da suke yi da 'yan IS masu ikirarin jihadi
Wata majiyar 'yan sanda ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewar tarin makaman na wata kungiyar 'yan bindiga ce, kuma makaman sun hada da gurneti da rokoki.
Gwamnatin ta ce ana kan bincike domin gano abin da ya sa ma'ajiyar makaman ya fashe, amma wani rahoto ya ce an yi imanin cewar ya faru ne a lokacin da ake son a kai makamai wata motar da aka ajiye kusa da wurin.
Hotunan da aka dauka bayan fashe-fashen sun nuna cewa fashewar makaman ta daidaita masallacin tare da lalata gidajen da suke kusa da kuma wasu gine-ginen.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#BBC
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI