Majalisar dokokin kasar Uganda ta
amince da wata sabuwar doka wadda za ta fara cajan 'yan kasar da ke
amfani da shafin sada zumunta na WhatsApp harajin shlillings 200
(kimanin naira 20) a kullum.
Dokar za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yulin bana.
Sai dai wadansu 'yan majalisa uku sun nuna adawarsu ga sabuwar dokar, inda suka bayyana sabuwar dokar da "karabar haraji kashi-kashi," kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.
'Yan majalisa Robert Kyaggulanyi da Joshua Anywarach da kuma Silas Aogon sun ce karin haraji zai zama wani take 'yancin masu amfani da WhatsApp saboda ana cajansu haraji kan katin wayar da suke saya.
Dan majalisar Arewacin Kasanda, Patrick Nsamba na jam'iyyar adawa, ya ce:
"Abu ne mai sauki dan majalisa ya ce harajin kaso 1 cikin 100 kudi ne kadan, amma ga mutanen da suke samun kasa da dala a rana, kudi harajin kudi ne mai yawa."
A galibin kasashen duniya ba a biyan haraji kafin amfani da kafar sada zumunta ta WhatsApp.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#BBC
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI