Kebbi: Dalili da ya sa Mujallar ISYAKU.COM bata aiko labarai na zaben jam'iyar APC ba daga Abuja

Mujallar ISYAKU.COM na ba jama'ar jihar Kebbi masoya kuma wadanda suka dogara ga labaranmu da ya shafi lamarin jihar Kebbi hakuri kan rashin samun halartar taron zaben shugaban jam'iayar APC na kasa da yake gudana a Abuja balle mu ruwaito maku rahotun gaskiyar lamari da ke faruwa.

Da farko dai wakili kuma 'dan jarida da ke taimaka mana wajen aiko labarai irin wannan idan ta samu daga Abuja bai koma Abuja ba bayan shagalin Sallah. 

Muna shaida maku cewa ISYAKU.COM Mujalla ce mai rijista da Corporate Affairs Commission karkashin kampanin Seniora International Ltd Rc 1470216 tare da samun albarkar ma'aikatar watsa labarai na jihar Kebbi, watau Kebbi state Ministry of Information and Culture.

Amma sakamakon matsaloli da barazana da Mujallar ke samu daga wadansu makiya ci gaban jihar Kebbi, basu yi ba, mun yi , amma basu son lamarin ya yi tasiri. Sakamakon haka muke haduwa da kalubale na munafunci, sharri, barnar suna, kazafi, cin amana, tozarci, raini, tare da yi mana kafar angulu a duk wurare da ake zaton tasirin aikin mu zai bayyana.

Babu hannun gwamnati ko jam'iyar APC na jihar Kebbi wajen tafiyar da Mujallar ISYAKU.COM ko KEBBI24.COM wanda, sakamakon haka babu tilas a kan mu dauki nauyin lamari da ba'a gayyace mu ba. Amma idan a cikin garin Birnin kebbi ne, mukan dauki nauyin tafiyar da wasu labarai kamar yadda muka saba, ba wai domin gwamnati ko jam'iyar APC na jihar Kebbi ba kawai, amma domin jama'ar mu ta jihar Kebbi da ke bukatar labarai masu inganci da babu bangaranci a ciki.

Dangane da tambayoyin ku kan lamarin APC a Abuja a yau, ina tabbata maku cewa yanzu haka Mujallar ISYAKU.COM ta sami sakonnin mutum 912 wadanda ke tambayar mu cewa sun ji shiru bamu ce komi ba. Haka zalika lokacin zaman shari'ar Gwamna Atiku Bagudu wata da ta gabata, mun sami sakonnin mutum 3884 da suke tambayar cewa basu ji komi ba daga Mujallar ISYAKU.COM kan labarin gaskiyar abin da ake toyawa a Kotu.

Muna ba masu karatun Mujallarmu hakuri, idan Allah ya yarda za mu inganta tare da fadada taskar wakilan mu na Turanci da Hausa, domin yanzu haka kayakin mu na aiki da ya shafi kamarar bidiyo da sauran na'urorin daukar sauti su iso kuma har mun fara amfani da su. Abin da ya rage shi ne ku taya mu addu'a domin Allah ya bamu sukunin wadatar da ku da labarai da suka shafi jihar mu tare da labaran al'ajabi da afadakarwa domin nishadantar da ku.

Mun gode,
Daga Mawallafin Mujallar ISYAKU.COM
Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN