Ana cigiyar wannan bawan Allah da hotonsa ya bayyana a wannan labari mai suna Malam Idrisa. Ya ce shi dan garin Alfagai ne da ke Birnin kebbi a nan jihar Kebbi. An sami wannan mutum ne a gidan wani hamshakin Malamai a kasar Sudan mai suna Sheikh Sala wanda ke zaune a jihar Kasala na kasar Sydan.
Malam Idrisa ya bar gida Najeriya da niyyar zuwa aikin Hajji da kafa, jin cewa ana zuwa
acewar sa yataso ne daga garin Alfagai dake Birnin Kebbi a
tarayyar Nigeria yau kusan shekara daya da wani abu, da niyyar zuwa
aikin Hajji kamar yanda ya samu labarin cewa ana iya zuwa ta mota, to
amma yace ya taho ne ba tare da sanin 'ya 'yan sa ko wani daga cikin 'yan
uwan sa ba domin ya san ba zasu bar shi ya taho ba, wanda shi kuma babban
burinsa kenan a rayuwa, ya gana da Dakin Allah.
Wannan bawan Allah ya ambaci wasu cikin yan uwansa kamar
Sarkin Zabarmawan Lagos Alhaji Ibarahim da kuma 'ya'yansa da ke garin
Alfagai kamar: Fatima da 'yan uwanta.