Kebbi: Wani babban jami'in Gwamnatin Bagudu ya umarci isyaku.com ya kwashe kayansa ya bar jihar Kebbi

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 29-6-2018


Da misalin karfe 3:31 na ranar Juma'a, Isyaku Garba Mawallafin Mujallar isyaku.com ya sami kira daga lambar wayar wani mai taimaka ma wani babban jami'in Gwamnatin jihar Kebbi, ya ce shi wannan jami'in ya ce isyaku.com ya tattara nashi kayaki ya bar jihar Kebbi kafin su iso jihar Kebbi daga Abuja bayan zartar da hukuncin Kotu a kan shari'ar Atiku Bagudu da Bello S.Yaki.

Shi dai wannan P.A da uban gidansa da muka sakaya sunansu a yanzu, ya ce akwai wani labari da muka wallafa ranar Alhamis wanda muka sa hoton kofar shiga gidan gwamnatin jihar Kebbi, da ma duk wani labari da muka wallafa ranar jajibirin shari'ar cewa bai yi ma wasu mukarraban gwamnati dadi ba.

 Wani abin mamaki shi ne, wai don Allah a ina wani Gwamna ko mataimakin Gwamna ya taba koran 'dan asalin jiharsa daga fadin jihar kawai saboda ra'ayi ko jin santin iko da buguwar barasar mulki ?.

Ina sanar da masoya wannan shafi cewa su kula kuma su sani duk wani abin da ya faru da isyaku.com wannan bawan Allah na da hannu a ciki.

Wannan bawan Allah dai bai taba yaba wani alhairi ko kwazo da isyaku.com ya nuna ba a jihar Kebbi, ta hanyar kirkiro ababe da dama da suka haifar da madogara ga matasa da al'ummar jihar Kebbi ta hanyar dogaro da kai, ciki kuma har da samar da Kampani da ke horar da 'yan jihar Kebbi a kan yadda ake sarrafa ingizon mahaja da silasilar wayar salula a jihar Kebbi.

Wani bincike da muka gudanar game da wannan bawan Allah daga nan isyaku.com wata biyar da suka gabata, ya nuna cewa wannan mutum yana daya daga cikin 'yan siyasa da suka fi bakin jini a cikin mazabarsu . Amma muka danne labarin bamu wallafa ba saboda murubar Gwamna Atiku Bagudu tare da hangen nesa bisa manufa ba wai mun kasa ne a aikin mu ba.

Bayan haka kuma, isyaku.com shafi ne da ya dauki ma'aikata da tsari da kowa zai amfana, bayan haka muna alfahari da cewa mu ne kafa ta farko mai zaman kanta da ta fara watsa labarai na jihar Kebbi a yanar gizo a tarihin jihar Kebbi wanda ba ko sisin gwamnatin jihar Kebbi a ciki.

Mun nuna goyon baya tare da yi ma gwamnatin jihar Kebbi da'a da biyayya har fiye da shekara uku, kuma muna gani kiri-kiri yadda ake yi mana danniya, wulakanci, cin fuska da rashin kulawa a karkashin wannan gwamnati, amma muka daure domin mun yi imani da shugabancin Sanata Atiku Bagudu, domin mun gane cewa wadanda ke irin wannan sharholama da bazar Gwamna Bagudu suna yi ne ba tare da sanin shi ba, kuma bai sani ba wanda haka ke bata siyasar wannan adalin Gwamna.

Duk abin da muke yi muna yi ne domin ci gaban jihar mu ba wai domin wani da ya samu dama karkashin mulkin Gwamnan adalci Sanata Atiku Bagudu ba, kuma domin bai sha wahala ba a siyasa yana neman ya bata ma Gwamna Atiku Bagudu siyasar shi ta hanyar neman ya kori 'dan asalin jihar Kebbi daga jihar Uwarsa ta haihuwa. Tabbas dama can wannan bawan Allah makiyi Gwamna Atiku Bagudu ne, wanda ke nuna yana son sa a fuska amma na ciki na ciki.

Isyaku Garba na isyaku.com bai yi lafi ba, domin mun rubuta labarai wadanda suka yi wa gwamnatin jihar Kebbi dadi fiye da shekara uku kuma a babu ko sisin gwamnati a cikin tafiyar da lamurran mu, ba a taba cewa an gode ba, amma saboda labari daya da ba'a lurar da mu cikin mutuntawa cewa muna kokari ba, sai kawai a ce mu kwashe namu da namu mu bar jihar Kebbi kafin wani ya dawo daga Abuja ?

Tarihi ya tabbatar cewa akwai wadanda suka ci mutuncin manyan jami'an gwamnati har da mai girma Gwamna Atiku Bagudu karara a Social Media, musamman kafar Facebook, amma Gwamna bai ce su a kama su ko su kwashe kayansu su bar jihar Uwaye da kakanninsu ba , watau jihar Kebbi.

Gaskiyar lamari shi ne ba zamu je ko ina ba, kuma duk wanda baya son ci gaban jihar Kebbi ta hanyar wulakanta mutane masu hazakar ciyar da ita gaba shi ne zai kwashe nashi da nashi ya bar gidan mulki idan lokaci ya yi tunda gidan haya ne mai alfarma, ba wai gidan da ya gina da kudinsa bane.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN