• Labaran yau


  Amurka ta sharara karya game da adadin farar hula da ta kashe a Siriya - Amnesty

  Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa, alkaluman da Kawancen Kasashen Duniya da Amurka ke jagoranci suka fitar game da adadin fararen hular da suka kashe a garin Rakka na Siriya ba daidai ba ne.

  Kungiyar ta ziyarci wurare 42 da aka kai wa hari a Rakka tun bayan fara kai hare-hare a garin kan 'yan ta'addar Daesh a watan Yunin shekarar 2017 inda suka gano an kai wa fararen hula da dama hare-haren bam.

  Kungiyar ta ce, hare-haren da Kawancen Kasashen da Amurka ke wa jagoranci suka kai ta sama a Rakka inda 'yan ta'addar PYD/YPG reshen PKK kuma suka kai ta kasa ya saba wa dokokin kasa da kasa na kare hakkokin dan adam.

  Kungiyar ta Amnesty International ta zargi Amurka da kin kare fararen hula a lokacin da ta ke kai hare-haren.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Amurka ta sharara karya game da adadin farar hula da ta kashe a Siriya - Amnesty Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama