• Labaran yau


  Dutsen Kilauea mai aman narkakkiyar wuta na ci gaba da barazana ga Amurkawa

  Dutsen Kilauea da ke ci gaba da aman narkakkiyar wuta a jihar Havaii ta Amurka ya cinye gidaje 117. 

  Wata daya da ya gabata ne dutsen ya fara aman narkakkiyar wuta da bakin hayaki inda ya zuwa ranar Juma'ar da ta gabata aka bayyana ya cinye gidaje 87.

  Amma ba a bayyana ko adadin g,idaje nawa dutsen ya ke wa barzana ba.

  Sakamakon fara aman wutar an kwashe dubunnan mutane daga gidajensu a yankin Puna.

  Kwararru sun ce, ruwan narkakkiyar wutar da dutsen ke fitarwa ya kai nisan kilomita 20.

  'Yan sanda sun sanar da jama'ar yankin da dutsen ya ke da su bar wajen in ba sa so ya rutsa da su.
  Ana kuma samun girgizar kasa na da can a yankin.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  #TRT 
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dutsen Kilauea mai aman narkakkiyar wuta na ci gaba da barazana ga Amurkawa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama